Ni Da Abokin Baba Na Hausa Novel's 1 To End @Baba Mono Haxor

A nutse nayi sallama dakin Daddy na, dakin a shimfide yake da tattausan carpet sakar hannu kirar kasar India, ruwan hanta ne kamar yadda jeren kayan dakin suke.  A hankali na zauna a kusa dashi ina kallon yadda yake sarrafa laptop dake hannunshi cikin kwarewa, ganin bashi da niyar dawo da hankalinshi gare ni, dama dai nasan halin baba in dai yana aiki baya maida hankalinshi ga kowa har ni er gaban goshin shi kuwa har sai ya gama. Remote na dauka na canza channel daga sports zuwa Zee World. Na ma manta ranar suna shirin da nake nacin kallo, Love Look Like What You Made Me Do.  Dan Murmushi nayi nace woah, ni na ma manta da shirin nan. Daddy ya dan yi glancing din wajen da nake zaune ya kafin ya maida hankalinshi ga laptop dinshi. A takaice har aka gama shirin suka fara tallace-tallace Daddy bai gama abinda yake yi ba. Ba a jima ba naji na fara hamma, remote na dauka na mayar mishi da tashar da yake kallo na mike, daidai lokacin daya rufe laptop din nashi ya kalle ni cike da kulawa. "Uwata, ya aka yi ne?" sunan mahaifiyar shi gare ni shi yasa yake kirana da Uwata, su Mommy kam Ummi suke ce min. Baki na turo cikin dan jin haushi nace "ni barci nake ji..... Sai da safe!" er dariya yayi ya kamo hannuna ya rike ya janyo ni na koma kusa dashi na zauna ina kara tura baki na. Kumatu na ya dan ja, "ohhh m soooo sorry princess, na tsaida ki koh? Akwai muhimman bayanai dana tura ne yanzun shi yasa, ayi hakuri. Gobe zamu je mu sha ice cream ni da princess dina, are we good now?" kaina na kawar daga kallonshi, yasa hannu ya juyo da fuskata zuwa gare shi, "hey, m trying to pay for what I did, aren't we good yet?" bansan lokacin dana yi er dariya ba ganin yadda yayi da fuskarshi, Ina son babana fiye da tunaninku saboda yana sona sosai, kaunar da yake min ko mahaifiyar data haife ni bata nuna min kwatankwacinta. Ban sani ba ko don hakan yana da nasaba da cewa ni Kadai ce diyar su??. Kai na girgiza ina dan murmushi, "naji na hakura, but we will also go for shopping, agree??" ya gyada kai, yes. Tashi tsaye nayi nace to sai da safe Daddy. Murmushi yayi, ki tashi lafiya Uwata. A main parlour naci karo da Mummy, da alamun turaka zata tafi ganin yadda taci kwalliya, ba wai ta fuska ba, ta jiki sai tashin kamshi take. Murmushi nayi naje na rungumeta, "Mommy sai da safe!" bayana ta dan shafa, "OK, sweet dreams baby" ta sake ni ni na wuce dakina ita kuma ta tsaya tana kashe wutar falon.         Ina shiga dakina wuta na kunna na shiga zare kayan jikina daya bayan daya, towel na zara na daura a jikina na fada toilet din dake manne a dakina. Cikin bathtub na shiga na zauna bayan na tara ruwa mai dumi, ban jima a ciki ba na fito. A cikin toilet nayi shafe shafen da zanyi, na fito. Kayan barci na saka marasa nauyi, kayan dana bari a tsakar daki na tsince na watsa cikin kwandon da nake tara kayan datti don nasan idan na bari Mommy ta gani gobe sai raina ya baci. Mommy mace ce mai tsabta da bata jurar kazanta ko ta anini. Kan katoton gadona nayi tsalle na haye kamar wata karamar yarinya, wayana na cire daga jikin socket na kunna data, social media na shiga na fara chat da friends dina. Ban samu barci ya dauke ni ba sai wajen karfe goma sha biyu na dare. Ban jima da fara barci ba naji numfashi ya fara min wahalar shaka, rigar jikina na fara adjusting daga jikina, ji nake kamar ita ta shake min wuya na kasa numfashi. Daga karshe tashi nayi gabadaya na cire rigar na jefar kasan gado na koma na kwanta. Dama don dole nake saka riga idan zan kwanta saboda fadan Mommy, ban cika kwanciya da riga a jikina ba saboda a yawancin lokuta na kan ji kamar rigar na shake ni ne, ban sani ba hakan sabo ne ko kuwa hali ne ko cuta? Ban sani ba, n I don't give a damn akan lallai sai na sani.                     *☆☆☆☆☆* Kiran sallar asubahi a cikin kunnena da yake masallacin unguwar mu a jikin gidanmu yake. Na saki gurnani a hankali saboda barcin daya cika min ido, da kyar na samu na iya bude idanuna suna komawa suna rufewa, na dauki kusan mintuna biyar kafin na iya tashi zaune, gashin kaina daya tattare ya barbaje min a fuska na tattara na maida shi baya, a hankali iska ya shiga kada sassan jikina hakan ya ankarar dani yanayin da nake ciki na babu riga, da sauri na dira daga kan gadon na dauki rigata na saka. Daidai lokacin Mommy ta leko, ganina a tsaye yasa ta maida kofar ta rufe ba tare da ta min magana ba. Sighing na danyi softly cike da jindadin bata kama ni ba. Bandaki na fada direct na dauro alwala, nazo nayi sallah na zauna Ina lazumi har sai da gari ya danyi haske, tashi nayi na fita daga dakina. Sai dana je na gaida Daddy sannan na shiga kicin inda na samu Mommy da Mama Sauda wadda take taya ta en aikace-aikace suna ta kokarin hada break fast, a nutse na gaida su sannan nima naje na kama musu. Muna gamawa na koma daki nayi wanka na fito, na bata lokacina sosai wajen fente fuskata da nau'in kayan kwalliya Kala-kala kamar wadda zata je biki. Sai dana gamsu da kwalliyar fuskata sannan na tashi na bude wardrobe dina wadda take shake da kaya kamar na mutane biyar ko fi. A hankali nake kare musu kallo har idanuna ya sauka akan wata atamfa cote d'voire ruwan coffee wadda aka mata zane da peach da yellow a jiki, dinkin riga da siket ne. Siket din pencil ne sai rigar doguwa don ta kusa kai kin gwiwa, ita kuma dinkin ya kama ni cif daga kirjina, daga uku ne ya saki sosai yayi baza. Ina gama saka kayan nayi simple daurin dan kwali, na dauko gyale mai dan fadi peach color da er karamar jakar vincci na rataya na fita bayan na dauki wayar hannuna da takalmi coffee color mai dan tudu. Akan dinning na samu Mommy da daddy har sun fara karyawa, duka kallona suka yi ganin yadda naci kwalliya cike da alamun tambaya. Kujera naja na zauna a kusa da daddy ina kallonsu, "School zan shiga in amso IT letter na daddy"  daddy ya gyada kai yaci gaba da cin kosan shi yana korawa da kunun gyada mai gardi, nima kunun gyadar na tsiyaya a cup na bude nadarar peak na kara a ciki na fara sha. A nutse muka gama cin abincin, na tashi na dauki jakata tare da yafa gyalena Ina kallonsu, "Mom, Dad, zan wuce sai na dawo" mom tace Allah ya kiyaye, daddy yace "ko dai in sa driver ya kaiki tunda ba jimawa zaki yi ba?" kai na girgiza, noo daddy, zan bi bus kawai. Ya gyada kai, "kudi pa?" nan ma kai na girgiza, "I've enough money wit me daddy" nan ma kai ya gyada, "OK, take care baby" Murmushi nayi na juya na fita cike da jindadin yadda iyayena suke kulawa dani, ta kowane fanni ni kam sai dai in godewa Allah daya bani iyaye kamar su. [12/9, 8:26 PM] ‪+234 816 965 3238‬: *NI DA ABOKIN BABA NA....!!*                       ©JeedderhLawalS                             *02*        Bus na hau directly har kofar gate din  KadPoly inda anan nake karatun Diploma na akan Science Lab Tech. Kasancewar an tafi hutu makarantar babu mutane sai tsilli-tsillin wadanda basu tafi hutu ba kawai, a hankali nake takawa har cikin ofishin IT coordinator namu na karbi IT letter na na fita. Hostel din mata na wuce daga can dakin kawata Ramla don nasan bata tafi hutu ba, ila kuwa, Ina sallama cikin dakinsu muka ci karo da juna. Cike da doki muka rungumi juna muna juyi a tsakar dakin kafin daga karshe muka dire a Kan gadonta muna dariya. Kallona tayi tun daga sama har kasa har sama, ta gyada kai tana er dariya, "inye diyar daddynta! Wannan fresh haka kamar wadda aka wanke da inji?" duka na kai mata a cinya Ina dariya, "ke ba baki da mutunci Ramla, duk uban kashin wannan dana tara a wuya zaki ce wai nayi fresh?" sai da muka gama shakiyancinmu na abokai sannan na kalleta, "ke ni ba wannan ba, ya zancen inda zamu je muyi IT ne don ban karbi letter na da wuri ba ban sani ba cikin wajajen da suka bamu ko zan samu?" Ta girgiza kai, "duk an cika a wajen pa gaskiya babu, nima tun last week na kai nawa suka ce wae an cika" fuskata ta dan yamutse, "lallai! Ya zanyi kenan?" kafada ta daga, "oho! Bake wae dadi gida ba kinje kin zauna kina hutu ba? Gashi next week zamu fara. Ni a Kano zanyi nawa" na kalleta "Kano? A Ina??" "cikin BUK, kin san Aunty Habi tana aiki da Lab dinsu, shine tace in je can inyi kawai. Har an kai letter sunyi accepting. Abinda ya shigo dani makarantar kenan na kawo accepting letter din" shiru nayi ina jijjiga kai, "Ramla ko dai nima can zanje inyi nawa IT din kawai? Nasan mawuyaci ne in samu waje anan" ta kalleni, "wa kike dashi a Kano?" nace oho! Daddy yana da mutane da dama acan, nasan ba za a rasa ba. Idan can dinne sai in dinga zuwa weekend gida..... Zan tambayi daddy inji dai tukun. Yaushe zaki tafi Kanon?" "ranar assabar kila" ta bani amsa. Na gyada kai kawai. Kayanta na tayata hadawa, tare muka fito da ita na janyo mata trolley ita kuma tana jan karamar jaka. Muna tafe muna hira da ita har bakin gate, anan muka ci karo dashi, My Crush!. Wata irin farinciki da murna suka rufe ni, Ya Allah ji nayi kamar in daka tsalle. Ta gaban mu ya wuce without glancing at us, duk yadda naso in daure kasawa nayi, ban san lokacin dana kira shi ba. "Muneer!!" cikin wata iriyar murya mai kama da whisper, duk da haka sai daya dakata da tafiyar da yake yi ya juyo ya kalleni, Kai na sadda kasa ina jin wasu irin abubuwa na min yawo a jiki. Cikin siririyar muryar shi da zan iya cewa ita tafi daukar hankalina game dashi yace, "ohh Ummie, ya kike?" Murmushi na saki a hankali kaina a kasa, nace "lafiya qalau, ya karatu?" "Lau..." ya amsa, "....bari in wuce sai anjima..... By the way, I like ur dressing" bin shi nayi da kallo yana tafiya a nutse ina wani irin murmushi kamar kumatuna zasu hade da kunnuwana. Sai dana daina ganin kurar shi sannan na maida Kallona ga Ramlah wadda ta coge a gefe tana jifana da harara, murmushi kawai nayi tare da daga mata kafada naja trolley din nayi gaba. Tsaki taja ta biyo bayana, "wallah Tallahi Babe kina bashi haushi a rayuwa akan Muneer dinnan, kin rabe wa namiji yana yazga ki. Yanzu kaf fadin KadPoly waye bai san cewa kina crushing din wannan player din ba, abun haushi ma da alamun baya yi dake!" fuska na hade sosai. Abinda ke hada ni da ita kenan, kushe Muneer. Bata damu da yadda na hade fuska ba taci gaba, "haba babe, ki daina bayar damu mana. There r so many guys out there ciki da wajen makarantar nan dake karakaina akan ki, don Allah ki kyale wancan yaron. Ba son ki yake yi ba!" a fusace na kalleta, "yeah right! Ai dama ban ce miki yana so na ba koh? Hakan bai dame ni ba, inda rai da rabo, zan ci gaba da bibiyarshi kuma har sai ya so ni Ramlah! Idan hakan yana bata miki rai ki kauda idanun ki daga gare mu, dats all" Kallona ta tsaya tana yi kawai, ba wai yau muka saba irin wannan musun ba in dai akan Muneer ne, Kai ta girgiza a hankali tare da furta Allah ya ganar dake! Cikin gatse na amsa da Ameeen. Muka ci gaba da tafiya har bakin gate ba tare da kowa ya sake cewa komi ba, dama zuciya ce ta kowa a wuya, magana kadan sai ta tunzura mu. Muna fita bakin gate kowa yayi nashi bangaren, ita ta hau motar Abuja ni kuma na dau drop din tricycle har Unguwar Rimi. Lokacin dana isa gida karfe sha biyu na rana bata karasa ba, kayan jikina na cire na saka na shan iska marasa nauyi na tafi kicin. Tare da Mommy muka hada abincin rana, ta shiryawa daddy nashi a cikin wani katon Basket mai kyau har da wani kayata shi da roses. Wannan Al'adar tunda na tashi naga Mommy tana yin ta, Indai daddy yana gari to abincin shi daga gida ake kai mishi, ba zan boye ba, abin yana burge ni, ina da niyar yin wannan Al'adar idan nayi aure. Direba ta ba ya kai mishi ofishin kula da harkar shigi da ficin jirage ta jahar Kaduna inda anan ne yake aiki a matsayin President na wajen. Ni kam sallah nayi sannan na fito dinning din, tuwon semovita ne muka yi da miyar danyen kubewa wadda ta sha busasshen kifi da tantakwashi da man shanu sai tashin kamshi take yi, sai zobo mai sanyi Shina anyi decorating dinshi da fruits. Muna hira da Mommy jefi jefi muna cin abincin na gaya mata yadda muka yi da Ramlah game da IT dina, shiru tayi tana Kallona kafin tace "zaki iya kuwa Ummi?" er dariya nayi, "haba Mom! It's not like ban taba zaman Kanon nan bane. I will b fine, after all anan zan dinga yin weekend dina ai" kai ta gyada, "sai ki jira daddyn ki ya dawo".          Koda na fadawa daddy abinda ake ciki ya dan nuna damuwarshi akan gida da zan bari, yace "Uwata tafiya zaki yi ki barmu mu biyu ne a cikin gidan nan kamar mayu?" ni kaina kuma sai a lokacin naji jikina ya fara sanyi, a sanyaye nace to daddy ko dai zan bari ne sai shekara mai zuwa sai inje? dariya suka saki shi da Mommy, daddy yace "oh ma silly princess! M not that wicked da zan hana ki karatun ki, bari in kira Dr. Ibrahim abokina ne, lecturing yake yi a BUK sai muji yadda za ayi" muna zaune ya kira shi suka gama magana suka yi sallama, "wai yace zaki samu sai dai a microbiology lab din su" Murmushi nayi, "daddy kasan fa dama nace maka idan na gama wannan program din zan nemi microbiology a ABU" yace faduwa tazo daidai da zama kenan? Na gyada kaina Ina Murmushi. Yace gobe zan tura mishi letter din sai a kai, Allah sarki princess dina zan yi kewar ki!. Da dare kuwa kamar yadda daddy ya min alkawari muka fita, chicken republic muka je ya sai min gashin kaji muka tsaya a freeze center ya sai mana ice cream da tarkacen snacks muka koma gida. Tare muka zauna muka ci komi, sauran kayan mommy ta je ta adana su. Mun danyi hira dasu kadan har zuwa karfe tara da rabi, kafin na musu sallama na wuce dakina. Kayan barci nasa na kwanta a rub da ciki idanuna a rufe, daddy gaskiya ya fada. Tun yanzu nake ji kewar su tana dabaibaye ni, anya zan iya kuwa???! [12/9, 8:30 PM] ‪+234 816 965 3238‬: *NI DA ABOKIN BABA NA....!!*                       ©JeedderhLawalS                             *03*            Tun da muka gama hada breakfast na koma na kwanta barci, ban tashi ba sai wajen karfe goma na safe. Brush nayi na fita falo na karya, daddy ya fita wajen aiki. Dama dai Mommy full house wife ce, babu aikin da take yi. Shi yasa nace muku rayuwar auren iyayena tana matukar burge ni, Mommy tayi karatu har matakin masters akan Pharmacy amma daddy ya hanata aiki, duk wasu bukatu nata kuma ya dauke su ba kamar sauran mazajen yanzu ba da idan matarsu tayi karatu taki yin aiki sai labari yazo ya sha banban saboda ba zasu raba hidimomin gida tare ba. Wanka na shiga nayi, na fito na shirya cikin doguwar riga ta wani material grey mai dan nauyi, dinkin ya kamani tsam ya bi jikina, sai daga kasa ne ya baje sosai. Saboda yanayin kirar jikina dama ba wai kiba gare ni ba, er siririya ce ni amma fa Akwai kira, daga sama har kasa kam sai dai in gode Allah. Kalar fatar jikina baki ne, duk da ba wai can ba, zaku iya cewa chocolate color dai. Gyale na dauka na dora shi akan kafada ta na fita. Dakin mommy nayi knocking na shiga, tana zaune a gefen gado da dan littafin hisnul Muslim a hannunta. Kallona tayi na zauna a gefenta, a dan shagwabe nace "mommy dan Allah inje gidan Anty Uwani?" anty Uwani kanwar mommy ce, yaranta hudu duka maza, mun saba dasu sosai saboda zumuncin iyayenmu. Lokaci zuwa Lokaci na kan je can har in musu weekend. Mommy tace "kinga baki tambayi daddy dinki ba Ummie, babu ruwana pa!" kara shagwabe fuska nayi nayi nace "mommy da wuri pa zan dawo Allah" Kallona tayi na lokaci kafin ta gyada kai, "shikenan,  but kar ki kai yamma fa!" cikin murna na gyada mata kai. Cike da doki na tashi, har na fita na sake komawa, purse dinta na bude na zari dubu biyar na fita da sauri ina dariya, kallo kawai ta bini dashi. A Unguwar Rimi suke zaune, sai dana tsaya na sai dangin fruits a bakin hanya sannan na karasa gidan. A can na wuni sur, sai gab da magrib sannan ta sa direba da danta na biyu AbdulJalal wanda yake kusan sa'ana ne suka rako ni gida. Daddy har ya dawo, Allah ya taimake ni ban sha fada ba saboda Daddy baya son yawo ko kadan. Bayan sallar isha'i ina zaune ina kallon film din Kaabil daga cikin laptop dina Ramla ta kira ni, murmushi nayi da naga sunanta a jikin wayata, wato har ta gama fushin kenan?? Da er dariya ta na daga kiran, "Lauratu ya ne?" haka nake kiranta idan naso tsokana. Ina jin dan siririn tsakin data saki, "ke pa u r a prof a ruining mood din mutum wallahi, meye wani Laure kamar wata Goggo a kauyen kayau?" dariya na sheke da ita cikin tura haushi, hakan ya kara tunzura ta kuwa. Sai da na gama tsokanarta sannan na tsaya ina sauraronta, hakuri ta bani game da abinda ya faru ranar, nima hakurin na bata tunda dukanmu we are at fault. Daga nan hira muka hau yi da ita, mun share fiye da awa daya muna hira har sai dana gaji don ni dama can ba gwanar hira bace musamman ma hirar waya, sallama muka yi kowa ya ajiye wayarsa.       Da dare muna falon daddy mu duka muna en hirarraki, aka kira daddy a waya. En maganganu suka yi kafin ya ajiye wayar yana kallona, "Uwata kinji an karbi letter dinki pa!" ban san dalili ba, gabana ya fadi ras! Rasa abin cewa nayi kawai na tsaya ina kallonshi, yaci gaba, "ranar Sunday zaki tafi mun gama magana da Ibrahim din. Sai ki fara shiri koh?" jikina naji yayi sanyi sosai, kafin kace me! Hawaye sun fara min yawo a kumatuna, cike da damuwa daddy yake kallona, "Uwata lafiya?" kai na gyada mishi a hankali, "I just started missing u ne daddy!" Dariya ya saki yayin da mommy tayi murmushi, hannu na ya rike a tausashe, "ohh my loving princess.... We gonna miss u!" group hug muka hada kamar zamu yi kuka. Shirye-shiryen zuwa Kano na fara yi, hada tarkace, sallama da dangi da en abubuwa. Komi cikin sanyin jiki nake yin sa, wannan shine karo na farko da zanyi tafiya ta fiye da watanni uku. Daddy dinmu dan asalin garin Malumfashi ne ta Katsina, danginshi duk a Katsina suke zaune don haka mu kan je can idan mun samu hutu in musu kwanaki zuwa sati. Amma Ina jin wannan tafiyar ta banbanta, zuwa zanyi fa in zauna da mutanen da ban sani ba na tsayin watanni hudu zuwa biyar, a garin da ban sani ba duk da cewa mun yi zaman Kano na shekaru biyu, amma that was then, I think tun ina primary 5 ne??? Haka dai naci gaba da Shirye-shiryena har zuwa ranar Sunday. Sai wajen karfe biyar na yamma muka bar Kaduna, daddy ne ke jan motar, mommy na gefen shi ni kuma ina gidan baya. Tafiyar tayi min wani irin sauri, sai naga kamar muna tafiya ne akan iska ba kan kwalta ba. Cikin dan lokaci kankani mun isa Kano, unguwar Tal'udu muka wuce tunda anan gidan yake. Naji daddy yana ba Mommy labari game da abokin nashi, yace lecturing yake yi amma ba a staff quarters yake zaune ba, yace dan asalin garin Kano ne kuma yanzu haka yana neman kujerar dan Majalisa ne. Yaran shi uku da matar shi daya..., ni dai tunda naji yace yana harkokin siyasa na maida hankalina kan wayata, dan siyasa? Allah ya gani basu cika burge ni ba, ban son siyasa. Kugi na karshe da motar tayi a cikin garejin gidan ne, tun daga cikin mota nake karewa gidan kallo. Ba wai yanke hukunci kai tsaye ba, yanayin gidan tafiy kafin ace mallakin just a lecturer (sorry lecturers, m not underestimating ur payment or something). Gida ne hawa daya, parking lots din gidan cike yake da manyan motoci ba na wasa ba, ga bikes da kekuna ina ji na yaran shine. Daga nan kana iya hango wani dan karamin garden a can gefen gidan, har wani dan karamin wajen wasanni na gani. A hankali muka fito daga cikin motar, already wani da nafi kyautata zaton mai gadi ne ya fara kwasar kayana yana shiga cikin gidan dasu. Shi yayi mana jagora zuwa wani babban falo daya min kama da fadar uwargidan sarkin Kano, ya sha jere na wasu narka narkan leather seats kala biyu, farare da browns, ko wane jeren kaya yana da nashi dinning table, Plasma TV wadda zaka yi zaton zata cinye bangon falon saboda girmanta. Kafafunmu suka nutse cikin wani tattausan rug carpet kamar auduga, nayi iya bakin kokari na wajen ganin cewa ban hangame baki nayi kauyanci ba, maganar gaskiya ban taba shiga tsarraren falo irin wannan ba duk da cewa ba laifi nayi shige-shige a parlours da gidaje na manyan mutane, wannan kam looks extraordinary sosai. Kujera muka samu muka zaun 3 seats, ina tsakiyar su daddy, er aikin gidan ta fito daga kitchen ta gaida su daddy kafin ta shige wata kofa a cewarta zata kira madam. Ina jin lokacin da daddy yake gayawa Mommy ai Ibrahim din baya nan, yaje wani seminar. Ni dai ba baki, I was very nervous a lokacin. Mintuna kamar goma sai gata ta fito, Ya Allahu!! Meye wannan a gabana? Naji zuciyata tana tambaya lokacin da nayi tozali da matar. Don fari fa Akwai fari kamar Baturiya, kyawu ma Akwai shi Masha Allah, wata irin kiba marar fasali ne da ita. Lokacin data zauna akan kujera suna gaisawa dasu daddy sai naga ta shirge a waje guda kamar kayan wanki. Da kyar na iya saisaita kaina na dan zame daga kan kujerar na gaisheta, da er fara'ar ta ta amsa har da ambatar sunana, "Safeenah ko?" na gyada mata kai a hankali. Ta maida kanta gasu daddy suna er hira, idanuna suka ci gaba da wandering a cikin falon bana ma jin me suke fada. Aka kira magrib daddy ya fita sallah, ni da Mommy kuma muka yi a cikin falo don bamu samu albarkacin samun gayyata zuwa dakin matar gidan ba, kuma ba a nuna min inda zan zauna ba, karewa kayana ma suna nan baje a tsakiyar falon. 'yar aikin gidan muka tambaya ta nuna mana bayi dake nan cikin falon muka shiga muka dauro alwala, motar daddy naje na dauko prayer mat muka shimfida anan muka yi sallah abinmu. Daddy yana dawowa daga sallah yace mommy ta tashi su tafi, nan fa idanuna ya raina fata da naga Mommy ta yiwa er aikin gidan magana akan taje ta gayawa matar gidan zasu tafi, idanuna suka yi raurau kafin kace me na fara hawaye shabe-shabe. Ba a dauki mintuna biyar ba sai gata ta fito tana taku da kyar, ban sani ba na takama ne ko kuwa dalilin kibar ta ne? Sallama suka yi dasu ta koma daki abunta. Hannuna mommy ta kama na musu rakiya har bakin motar su, zuwa lokacin kam kuka nake har da shessheka, suka saka ni a tsakiya suna lallashina har na samu kukan ya lafa. Ina nan tsaye suka shige mota suka ja suka tafi bayan na sha nasihohi daga gare su. Na bi bayan motar nasu da kallo har suka bar gidan aka maida gate aka rufe, na maida kallona ga dankareren gidan da zan rayu a ciki zuciyata cike da tarin damuwa iri-iri, daga can kasan zuciyata ina jin wata irin nadama na dabaibaye ni, Me ya kaini???? A hankali wasu siraran hawaye suka biyo kan Kumatu na.....! Just want to say thank u for those following me, commenting and voting on this story. Please keep it up, keep voting, comment, and share it with your friends......                           T [12/9, 8:32 PM] ‪+234 816 965 3238‬: *NI DA ABOKIN BABA NA....!!*                       ©JeedderhLawalS                             *04*          Sai dana kwashe lokaci mai tsawo a cikin farfajiyar gidan a tsaye kafin na samu kwarin gwiwar jan kafafuna da kyar na koma falon. Ina shiga na ci karo da er aikin gidan wadda saboda tsabar wata irin shiga mara fasali da tayi yasa na kasa gane ko wace irin yare ce, cewa tayi in zo muje ta nuna min dakin da zan kwanta inji madam dinta, babu musu na dauki jakar hannuna na janyo daya daga cikin jakunkunan dana taho dasu nabi bayanta bayan itama ta dauko wasu. Abinda na kula duka dakunan gidan a falon kasa suke, ni tunda nazo ban ga kowa ya hau saman ba. Wani dan madaidaicin daki cikin jerin dakunan dake cikin falon ta bude muka shiga ciki. Dakin yana da fadi ba laifi, Akwai toilet a ciki ga wani medium size gado ruwan golden, mirror da closet sai er karamar sofa da study table. A tsakiyar dakin an malala wani tattausan circle carpet baki, sauran dakin kuwa malale yake da wasu en ubansun marbles fari da gold, well, ba laifi ya burge ni sai dai yadda aka tsara dakin ne sam bai min ba. A raina nace sai na canza shi. Ina ta karewa dakin kallo har ta gama shigo min da kaya na duka, ta tambayeni idan Akwai abinda nake bukata? Kai kawai na girgiza mata tare da mata godiya, ta min sai da safe ta wuce abinta. Jakar hannuna na jefa akan gado na samu gefen gadon na zauna Ina kara karewa dakin kallo, tashi nayi na leka toilet, Shima babu laifi ya hadu, na dawo na bude closet din babu komi a ciki sai er guntuwar kura data yi, tsumma na lalubo na goge ta tas na lalubo turaren kaya a cikin kayana na watsa a gefen closet din kafin na fara shirya kayana a ciki, sai dana cika ta tsil da kaya wasu ma da kyar suka shiga, na makare kan mirror na da tarkacen kayan shafa dana kwalliya da nau'in perfumes kamar a wani dan karamin super store. Sallar isha'i nayi na hada da shafa'i da wutiri, ina gamawa naji wayana tana kara, ringing din dana sakawa daddy ne. Da sauri na tashi na daga kiran, gaisawa muka yi ya fada mun sun isa gida lafiya, mun danyi hira kadan yaba mommy wayar itama muka dan yi hira, sai data kara min da en nasihu akan wadanda ta min sannan muka yi sallama na ajiye wayar. Ruwa na watsa a jikina na nemi kayan barci marasa nauyi na saka na kwanta, amma kwata-kwata barci yace bai san idanuna ba, tunanika iri-iri suka dinga min yawo a kwakwalwa, daga karshe waya ta na dauko na fada duniyar gizo. Washegari kamar yadda na saba da asubahi na tashi nayi sallah, shiru Ina kan abin sallah a zaune ina debating akan in fita in taya matar gidan aiki ko kuwa in zauna a daki? Daga karshe dai kawai na tashi na fada wanka, usual ways din harkokin rayuwata na bi, kwalliya data kwashe ni kyawawan mintuna talatin, minti ashirin na fiddo kayan sawa da shiryawa, zuwa lokacin dana tsaya a gaban dogon yaro ina sake duba kaina, karfe bakwai da mintuna ashirin. Cike da tunanin yadda zan karasa cikin makarantar BUK na fito falo, babu kowa  a cikin falon amma na jiyo motsi a can wata kofa dake gefen dakin matar gidan. A hankali na karasa tare da lekawa, hangame baki nayi kamar zai rabe biyu. Wani dankareren kicin dana gani wanda zan iya cewa ya lunka dakina sau biyu, kayan electronics na kicin babu kalan wanda babu. A gaban gas cooker na hangi er aikin gidan tana soya plaintain, karasawa wajenta nayi muka gaisa cikin girmamawa, na tambayeta matar gidan tace min wai bata tashi daga barci ba, Kai na gyada cike da mamaki. Wace matar aure ce ke kai karfe takwas na safe saura tana barci?? Tambayarta nayi yadda zan isa wajen IT dina, tace ai Direban da zai kaini yana waje yana jirana, tun dazu yayi magana. Juyawa nayi na fita, daga kicin din tace min breakfast fa? Nace mata zanyi acan. A farfajiyar gidan na hangi direban, a mutunce na gaida shi ya bude min gidan baya na shiga yaja motar muka wuce. Mintuna talatin mun shiga cikin BUK, har gaban microbiology lab muka je yayi parking, tare dashi muka shiga lab din ya samu lab attendants suka yi maganganun da zasu yi, ya tafi ya barni bayan ya fada mun lokacin da zai dawo ya dauke ni. Ina zama sai ga Ramla sun shigo ita da Antin ta, nan muka rungume juna cike da murna, itama Anty Halima tafiya tayi ta barmu anan. Da yake ranar farkonmu ce a wurin babu wasu ayyuka da muka yi, wajen karfe goma sha daya muka fito ni da ita zuwa Cafeteria din dake cikin department din. Tafiya muke yi a hankali, tsarin makarantar ya burgeni kwarai, er hira muke yi da ita game da wajen har muka shiga cikin cafeteria din, babu students sosai zama kawai muka yi muka yi order din abinda zamu ci. Muna gama cin abincin lab muka koma, lab attendants din were very friendly don haka cikin dan kankanin lokaci muka saba dasu. Wadanda suke yin aikin project dinsu sun kawo ayyuka, nan ne fa muka tashi muka fara aiki. Sai wajen karfe biyu muka tashi, wani dan karamin garden muka zauna muna ta hirarmu ni da ita ina jiran Direba yazo tunda ita sai ta jira Anti Halima ta gama ayyukanta, sai wajen karfe biyu da rabi sannan Bala Direba ya iso. Ina hango motar na gane ta saboda a cikinta muka zo. Da sauri nawa Ramla sallama na tashi nayi wajen da yayi parking, a mutunce na gaida shi na bude bayan motar na shiga.                        *♡Jeedderh♡* [12/9, 8:35 PM] ‪+234 816 965 3238‬: *NI DA ABOKIN BABA NA....!!* ©JeedderhLawalS *05* Wata kyakkyawar yarinya cikin kayan makaranta dogon wando navy blue da shirt fara ta dago kyawawan idanunta tana kallona, ban san lokacin dana sakar mata murmushi ba saboda tsananin burge ni din da tayi, a gaban motar kuma maza biyu ne suma cikin shigar kayan makaranta irin na yarinyar, duk suka juyo suna kallona. Zama nayi sosai a gefenta ina ta watsa musu Murmushi yayin da direba yaja motar, yarinyar da nake tunanin shekarunta zasu kai bakwai zuwa takwas tace min ke ce bakuwar da daddy yace zata zo mana gida? Na gyada kai ina kallonta, nice beauty, ya sunanki? Murmushi tayi, sunana Hafsah amma daddy yana ce min pretty Hafsey, su yaya Abdallah kuma suna ce min Hafsatu... Ta karasa tana pouting cike da shagwaba. Er dariya nayi tare da jan kumatunta, "kai amma Yaya Abdallah bai kyauta ba! Hafsatu ai sunan tsofi ne" ta gyada kai tana turo baki tare da kallon wanda yake kama da shine babban yayansu, "ai kullum sai na gaya mishi amma sai yace wae ai nima tsohuwar ce" na kalli yaron Ina Murmushi, "Yaya Abdallah baka kyauta ba gaskiya, tana yarinyarta ka dinga ce mata tsohuwa?" yaron yayi dariya, "sunan maman Daddy gareta pa, don Allah ba tsohuwar kenan ba?" daya yaron na gefenta ya kwashe da dariya, "tsohuwa ce mana, baka ga har ta fara furfura Akanta ba?" Hafsat ta kai mishi duka a kafadar shi, ya kauce yana mata dariya. Tsokanarta suka ci gaba dayi suna dariya har sai data fara kwalla sannan na tsaida su, "here, enough with the teasing, a kyale pretty haka nan ko?" ta gyada kai tana min murmushi, kanta na shafa ina jinta har cikin raina. Yarinyar tana da wani irin kyau duk da suma sauran yaran suna dashi amma ai kun san kyan mace ya banbanta dana namiji, ina mamakin inda ta gado shi a raina nace kila sai dai wajen mahaifinsu don babu mai kama da mahaifiyar su, dama dama dai Qaseem mai bin Abdallah, naga suna dan yanayi da Anti Mubeenah. Kafin kace me mun saba da yaran, dama ni bani da wahalan sabo suma naga hakan a tattare dasu. Muna isowa gida na dauki school bag din Hafsat ita kuma ta rike lunch box dinta, hannunta cikin nawa muka shiga falo ina taya ta miming din wakar twinkle little star. A daya daga cikin kujerun falon, Anti Mubeenah ce zaune ya harde tana duba jarida, yaran suka zube a gabanta suna bata labarin makaranta, sai dana bari suka gama hayaniyar su sannan na duka na gaida ta. Fuskarta dauke da dan murmushi ta amsa tare da ce min Akwai abinci a kicin, godiya na mata tare da cewa sai nayi sallah, dakina na wuce nayi sallah, na janyo wayata na kira mom don nasan daddy yana office ni kuma ban cika son kiranshi a wajen aiki ba, mun jima muna hira da ita kafin muka yi sallama, ana kiran sallar asr nayi na janyo system dina na kunna kallo tunda babu abinda zanyi, da a gida ne kila na shiga kicin ina taya mommy na girkin dare. Ina zaune anan ina kallo Hafsat ta shigo cikin kayan makarantar islamiya, na daga Kaina na kalleta ina dan murmushi, "pretty Hafsat an dawo ne?" ta zauna a gefena tana turo baki, "malam ya bamu aiki a makaranta kuma ban iya ba, gashi Abbu da yake koya min karatun baya nan" zama nayi sosai akan gadona nace bani littafin in gani, ta bude jakar ta ta miko min na duba, Tawheed ne, tambayoyi akan imani. Murmushi nayi na kalleta nace "yanzu dai je ki kiyi sallahr magriba tunda an kira, bayan isha'i sai ki dawo mu yi" da murnarta ta tashi ta tafi, har ta kai bakin kofa ta dawo da gudu ta rungume ni, "Aunty thank u" dariya nayi na bita da kallo har ta bar dakin, kai na girgiza na tashi na fada bandaki. Bayan sallar isha'i ina kan sallaya a zaune Qaseem yayi sallama ya shigo dakin, yace Aunty Nafeesah wae Mami tace kizo mu ci abinci, ba musu na tashi nabi bayanshi don dama yunwa nake ji. A kan dinning na samesu su duka suna cin abinci, gefen Hafsat naja kujera na zauna. Ganin kowa serving din kanshi yake yi yasa na dauki plate na bude flask din abincin, tuwo ne kaman na semovita miyar danyen kubewa, tunda naga miyar tsululu kamar ba danyen kubewa ba nasan cewa tuwon sai a hankali, Illa kuwa ina kai loma daya bakina da kyar na hadiye, tuwon gashi nan latab kamar danyen gari alamun bai gama dahuwa ba, miyar sai dan banzan yaji kamar da taruhu kadai aka yi ta, babu taste ko na anini sai shegen karnin kifi. Da kyar na iya hadiye lomar farko, ban yi kuskuren kai wata bakina ba don na tabbata idan na kuskure ta sake shiga bakina sai na amayar da dan guntun abincin daya rage a cikina. Su kansu na ga tsakura kawai suke yi, kallonsu kawai nake yi cike da mamaki. Ta ya za ayi mutane su rayu da irin wannan abincin a duniya? Koda yake yau ne karo na farko dana ci abincin gidan, ban sani ba kila rana ce ta bacewa mai girkin kawai, da wannan tunanin na gyada kaina na tashi daga kan table din bayan na wa Anty Mubeenah sai da safe. Dakina na koma naje nayi brush na wanke bakin da mouth wash, cikina wani irin hautsinawa yake yi saboda yunwa, jikar dana fita da ita dazu na bude, wata irin ajiyar zuciya na sake ganin Pack din cookies din New Yorkers, na manta dashi ma ni shaf dazu muka saye shi a cikin makaranta. Zama nayi akan gado na bude shi na fara ci, wayata na hannuna ina chatting, Hafsat ta shigo dakin. Tare da ita muka cinye cookies din, daga nan na koya mata aikin da aka basu, kallon film dina da nake kallo muka ci gaba dayi sai wajen karfe goma da rabi ta min sai da safe, na shafa kanta nace ki tashi lafiya pretty., kar ki manta pa kiyi addu'ar kwanciya barci kinji? Ta gyada kai, "thank u Aunty, sai da safe" na dan hade fuskata, "ohh pretty, sau nawa zan gaya miki bana son Aunty dinnan? Call me Yaya Nafee, bai fi dadi ba?" ta girgiza kai cikin tsokana, "babu dadi gaskiya" kofar dakin na nuna mata "oya, bi can sai da safe" ba musu ta tashi ta fita tana er dariya kasa-kasa. Tana fita na janyo wayata ina kallon screen din, a cikin messages nake ina shawara da zuciya ta akan abinda nake shirin aikatawa, daga karshe dai nayi typing, *"you sleep?"* na turawa Muneer, tsawon mintuna sha biyar babu amsa, na sake tura *"seems like you are, good night!"* na kashe wayar na dorata akan bedside table na kashe wuta tare da yin addu'ar kwanciya barci na kwanta. *♡Jeedderh♡* [12/9, 8:40 PM] ‪+234 816 965 3238‬: *NI DA ABOKIN BABA NA....!!* ©JeedderhLawalS *06* Nayi tunanin idan na tashi zan ga reply daga Muneer ko kuma missed call dinshi, sai dai har na gama shirina tsab babu shi babu alamun shi. Sai zuwa lokacin ne na fahimci imma dai yana sane yaki min reply jiya ko kuma yayi barci wulakanci ne ya hana ya biyo sahuna da safe, kwafa nayi ina jijjiga kai. Ranar ma dai abincin safen sai godiyar Allah, plaintain ne aka soya da shayi da soyayyen kwai, tsakani na da Allah nasan ba zan iya cin abincin nan ba, haka nan dai na dan tsakura har zuwa lokacin da Bala yazo muka dunguma gaba daya har su Hafsat muka fita. A mota daya muka tafi dasu, sai da muka biya ta makarantar su muka ajiye su sannan muka wuce. Da rana koda muka dawo bamu samu Anti Mubeenah a gidan ba, har dare bata dawo ba sai bayan isha'i likis sannan. A zaman sati dayan da nayi a gidan zan iya cewa zama ne na takura, if not for Hafsat dasu Abdul I didn't think I would've survived. ita dai matar gidan yadda na kula da ita, bata cika jan mutane a jikinta ba, ni dai tunda nazo gidan ban ga bare ya leko ba, makota ne, abokai ko dangi. Tsakanina da ita gaisawa ne kawai, idan mun hadu a dinning mu danyi hira sama-sama, ga yawo, idan ta saka Kafa ta fita daga gidan tun safe sai dare take dawowa duk da Hindatu mai aikinsu naji tace tana da saloon da take kula dashi. GA er aikinsu kuwa ban ma san me zan ce ba, ni ban ga dalilin da zai sa in dauko er aiki ba kuma ba zata min gamsasshen aiki ba in kyaleta duk da cewa ni har ga Allah I dont have any plan na daukar er aiki Ina nayi aure, ga Hindatu dai kam abin babu bayani, ita ba ga girki ba, ita ba ga gyare-gyare ba. Aikin data iya daya; ta sha kona sanwa idan ta dora ta fara kallo. A takaice dai kafin zagayowar ranar juma'a sai da naji Kano ta fita daga raina, ni ban saba irin rayuwar kadaici dinnan ba. Ranar juma'ar kuwa Ina dawowa daga wajen IT dama dan karamin kit dina a Shirye yake tsab, Anty ta fita yawon data saba sai sako na bari a wajen Hindatu nace tace mata na tafi weekend gida, dama Daddy ya turo wanda zai dauke ni, a farfajiyar gidan ma na dawo na tarar dashi yana jirana don haka babu bata lokaci muka wuce Kaduna. Sai wajen karfe biyar da rabi muka isa gida saboda yanayin go slow da muka samu a hanya kafin mu fita daga cikin Kano, da ihu na da komi na shiga gidan, kit dinma sai driver ne ya shigo min dashi. Mommy tana kicin tana girki ita kadai, na rungumota ta baya ina tsallen murna, juyowa tayi tana kallona cikin murmushi, "oh ni wannan yarinya tawa ban san yaushe zata girma ba" na buga kafa cike da shagwaba nace "mommy!!" dariya tayi ta rungumo ni jikinta cikin nuna kewa. Dakina na shiga an share min shi tass sai tashin kamshi yake yi, na cire kayan jikina na fita zuwa kicin na kamawa Mommy girkin, muna yi muna hira, yawancinta tambaya ce akan wajen da nake zaune, babu matsala dai ko? Kina cin abinci? Tambayoyi dai iri-iri. Muna nan Daddy ya dawo, har cikin kicin din ya shigo ya daga ni sama Cak yana juyi dani, dariya na saki na rirrike shi har ya dire ni kasa. Sannu da zuwa na mishi ya amsa yana shafa kaina, na amsa brief case din hannunshi na raka shi har dakin shi kafin na fito na barshi ya shirya. Bayan isha'i muna falo zaune akan babbar tabarmar cin abinci, hira nake musu, duk abinda nake yi a Kano babu wanda ban tsallake ba, su kuma suna sauraro cikin nuna rashin gajiyawa na dariya su yi, na mamaki kuma su jinjina kai. Ranar kam sai wajen karfe sha daya muka yi barci muna ta hirar yaushe gamo. Kwana na biyu a gida na koma Kano cike da kewar iyayena, ji nake kamar inyi zama na acan. Hindatu kadai na samu a gidan, tace yaran dama a gidan kakannin su suke yin weekend, ita kuma Anty Mubeenah tace wajen bikin kanwarta mawuyaci ne ma idan ba kwana zata yi a can ba, na jinjina kai tare da kwaso tsarabar fruits dana musu a hanya na shirya su a cikin fridge. Wajen karfe takwas na dare ina zaune gidan shiru babu motsin kowa, nasan da su Hafsat suna nan da yanzu suna dakin ko dai muna hira ko kallo ko kuma ina koya musu assignment. Horn din mota naji a bakin gate kafin naji karar bude gate, a raina nace Anty Mubeenah ta dawo kenan. Hasken motar ya ratso ta cikin windown dakina zuwa cikin labulaye na da yake window din dakin a kusa da garejin gidan take. Minti kamar biyar na bata na tashi na fita da niyar inje in mata sannu da zuwa. Tsaye a jikin fridge hannunshi dauke da gorar ruwan Sanah yana sha directly daga cikin gorar, hannunshi daya rataye da suit dinshi yana kuma rike da brief case. Dogo ne ba can ba, idan da ba don na sanshi a hoto ba to da zan iya rantsewa da Allah ince bashi bane, saboda ko a cikin hoton ban hangi yarintar dana gani a tattare dashi ba a lokacin, da nace yarinta ba wai ina nufin yaro bane, aah Ina nufin wanda bai kai girman daddy na ba; Abban su Hafsat ne. Wata irin gigicewa naji nayi, haka kawai naji kafafuna sun yi wani irin sanyi wanda ban iya daurewa ba sai dana dangana gwiwoyina da marble din dake malale a tsakiyar falon, ban sani ba tsabar kwarjinin da yayi min ne yasa gabana ya tsananta faduwa ko kuwa wani abu daban?? Cikin rawar murya nace "sannnnnu da..... Zuwa...... Abbbbuh!!".........
  @BABA MONO HAXOR


NameTelephoneTelephone
Haxor+2348108811856+2348106384398


FacebookBaba Mono Haxor
TwitterBabamono_haxor
Instagram
Babamono_haxor
Google +
Baba Mono Haxor
YouTube
Baba Mono Haxor

You may like these posts